Gwamnatin Amurka karkashin Shugaba Barrack Obama na shirin kakabawa kasar Rasha takunkunmi a matsayin martini kanshisshigi da kuma satar bayanan da ake zargin Rasha tayi a zaben shugaban kasan Amurka da aka yi a cikin watan da ya gabata.
Jaridar Washington Post tace ana ta tafka muhawara a fadar White House akan yadda za a gaggauta hukunta kasar Rasha, musammam ta hanyar anfani da dokar cikakken ikon shugaban kasa wanda shugaba Obama yasa ma hannu tun a shekarar data gabata.
Wannan dokar dai ta baiwa shugaba damar saka takunkumin tattalin arziki ga wadanda aka samu da laifin kutse, dake a wata kasar waje, jamiaan tsaro basa iya kaiwa gare su.