An Kaddamar Da Kungiyar Nakasassu Mabiya Jam’iyyar APC

Yayin da ake taron kaddamar da kungiyar nakasassu mabiya jam’iyyar APC, daraktan cibiyar demokaradiyya ta duniya International Republican Institute, na Najeriya, ya bayyana cewa suna aiki tukuru da kungiyoyin nakasassu na mata da matasa domin yi masu zagi su cimma muradunsu na siyasa.

An yi wannan yunkuri ne domin samawa kowa dama ne ya sami muhallin zama a tabaramar demokaradiyya da kuma kara hada huldar muradu domin nan gaba, a cewar daraktan.

Nakasassun sun yi cincirindo a shelkwatar jam’iyyar APC, inda suka bayyana cewa yawan nakasassu a Najeriya baki daya ya kai Miliyan 25, a cikin kimanin mutane Miliyan 170, na kasar baki daya, kuma sun bayyana cewa mutanen da suka kyautata masu kadai zasu marawa baya a babban zaben shekara 2019.

Musbahu Lawan Dede, shine shugaban kungiyar kuma ya bayyana cewa duk wasu shirye shirye da gwamnati ke gudanarwa a Najeriya, sai an sa naksassu a ciki domin irin gudummuwar da suka bada, wadda ta kai jam’iyyar ga nasara.

Jam’iyyar APC, mai mulki ta yi alwashin tallafawa nakasassun ta hanyar yaki da fatara da kuma tsayawa takarar mukamai kamar yadda sakataren jam’iyyar ya bayyana.

Ga cikakken rahoton Nasiru Adamu El-hikaya, daga Abuja.

Your browser doesn’t support HTML5

An Kaddamar Da Kungiyar Nakasassu Mabiya Jam’iyyar APC