Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Batun Ba Gaskiya Bane - Kukasheka


Kakakin Rundunar Sojin Najeriya janar Sani Usman Kukasheka
Kakakin Rundunar Sojin Najeriya janar Sani Usman Kukasheka

A dai dai lokacin da dakarun Sojojin Najeriya ke kammala rawar daji a dajin Sambisa, sai ga wasu bayanai a kafofin labarai a gida da wajen Najeriya, dake nuna cewa ‘yan Boko Haram, sun sake yin awon gaba da karin wasu mata ashirin da biyu a garin Fulka dake jihar Borno, bayan ayi zargin sun kai hari garin.

Rundunar Sojojin Najeriya ta karyata zargin, kakakinta janar Sani Usman Kukasheka, yace duk wanda ya fitar da wannan labarin makaryaci ne yana mai cewa bai san dalilin da yasa mutane suke yada abinda ba gaskiya ba ne.

Ya kara da cewa Fulka tana da kyakkyawan tsaro da kewayenta don haka maganar ba gaskiya ba ce “kuma muna ci gab da aiki daidai gwargwadon halidomin kiyaye rayuka da dukiyoyin jama’a ba a garin Fulka ba duk da sauran wurare da jami’an tsaro suka a yankin arewa maso gabashin Najeriya”.

Kakakin yace farfaganda ce ta ‘yan ta’adda saboda abin yakare masu shine suke neman su tayarda hakalin jama’a.

Hedkwatar Sojojin Najeriya ta yabawa Muryar Amurka bisa yadda take bada rahotanin tsaro irin wanna a Najeriya.

Wani masanin tsaro Air Commander Baba Gamawa, yace irin wadannan labarai na karya farfaganda ce na ‘yan ta’adda domin cusa tsoro a zukatan mutane domin nuna cewa suna da sauran tasiri.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG