Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawan Najeriya Ta Yiwa Dokokin Zabe Gyaran Fuska


Ginin Majalisar Tarayyar Najeriya
Ginin Majalisar Tarayyar Najeriya

Kawo yanzu karatun dokokin zaben Najeriya ya wuce mataki na ukku a Majalisar Dattawan kasar jiya

Sanata Abubakar Kyari wanda yake wakiltar arewacin Borno ya yiwa Muryar Amurka karin haske dangane da kudurorin dokokin da aka amince dasu.

Yace akwai wata shari'a da aka yi aka kawo batun naura mai bada bayanan kowane mai kada kuri'a wato card reader inda kotu tace naurar bata cikin dokar zabe. Yace yanzu sun sashi cikin doka domin yana da anfani. Naurar tayi tasiri a zabukan shekarar 2015.

Majalisar da kuma da hukumar zabe INEC ikon gudanar da zabe ta naurar kwamfuta wato "electronic voting", idan ta ga daman yin hakan lokacin da ta ga ya dace.

Doka ta ukku ita ce ta yin anfani da mashin a aika da sakamakon zabe nan take idan aka kada kuri'a zuwa matattara ba tare da sai an kaida takardu ba. Amma kuma yin hakan sai an tabbatar cewa mashin din babu wanda zai iya sauka sakamakon.

Akan batun rasuwar dan takara kamar yadda ya faru a zaben gwamnan jihar Kogi lokacin da dan takarar dake kan gaba ya zasu Sanata Abubakar Kyari yace yanzu an kara dokar da ta ba INEC ikon daukan mataki. Idan har an fara zabe dan takara ya rasu to INEC zata tsayar da zaben har na kwana 21. Zata tambayi jam'iyyar da dan takararta ya rasu idan tana son ta cigaba da zaben sai INEC ta amince mata.

Dokar kuma ta tilastawa hukumar zabe wajen yin anfani da naura mai kwakwalwa wajen kada kuri'a da tantance katin zabe. Nick Dazan babban daraktan watsa labarai na hukumar zabe yace a bangarensu suna marhaban da gyararn da Majalisar Dattawa tayi. Yin hakan zai kara inganta zabuka a kasar.

Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:45 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG