Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Kunar Bakin Wake Ya Kai Hari Maiduguri


A jiya da misalign karfe 11:00 na dare ne wani dan kunar bakin wake ya tada bom din dake jikinsa a kusa da wani gidan mai da ake kira Gujari filling station, dake cikin garin Maiduguri dake kan titin tashen motar Muna wanda akafi sani da “Muna Garage” inda ya kashe kansa, batare da ya taba kowa ba.

Kakakin rundunar ‘yan Sandan jihar Borno, DSP Victor Isoku ne ya tabbatr da afkuwar lamarin a cikin wani sako da ya aikawa manema labarai, inda yace an kuma sami tasahin wani bam din a wani kauye da ake Dusma a karamar hukumar Jere dake jihar ta Borno, inda nan ma dan kunar bakin waken ya kashe kansa ya kuma raunata wani mutun daya.

A ‘yan kwanakin nan dai ana samu tashin boma boman ‘yan kunar bakin wake tun lokacin da rundunar Sojan Najeriya ta bada sanarwar kakkape ‘yan kungiyar Boko Haram daga dajin Sambisa.

Irin wannan hare haren ‘yan kunar bakin wake dai yana cikin matsalolin dake addabar mutane masamman a yankin Maiduguri da kewaye ganin cewa irin wadannan mahara kan zo ne bazata su kuma afkawa mutane a wurin Ibada ko kuma a kasuwanni suka kashe duk wanda tsautsayi ya fadawa ko kuma su raunata shi batare da la’akari da mutanen dake wurin ba walau mata ko maza ko kuma kananan yara.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:39 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG