Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buratai Ya Jinjinawa Dakarun Najeriya Domin Kare Martabar Kasar


Janar Yusuf Tukur Buratai
Janar Yusuf Tukur Buratai

Rundunar Sojojin Najeriya, ta kammala gasat harbe harbe da gwajin makamai na shekarar 2017, wanda aka kaddamar a dajin Sambisa.

Manyan jami’an Sojojin Najeriya, da dama ne suka halarci gasar an dai kwashe kwanaki biyar ana gudanar da gasar da gwajin makamai. Rundunar Sojojin Najeriya, shiyya ta bakwai dake Maiduguri ita ta zo na daya.

Runduna ta tamanin da biyu dake jihar Enugu, ita tayi na biyu, runduna ta takwas dake karamar hukumar Mongono, a jihar Borno ita ta kasance ta uku, inda kuma aka mika masu kyaututtuka nay abo.

Hafsan Sojojin Najeriya janar Yusuf Tukur Buratai, ya bada kyautan Naira miliyan uku ga rundunar da tayi na daya a inda sanata George Akume, shima yaba rundunar Naira miliyan daya.

Rudunar da ta zo ta biyu shugaban Sojojin ya basu Naira miliya daya haka ma rundunar da tazo ta uku itama ta sami Naira miliyan daya.

Janar Buratai, yace yayi farin ciki ganin yadda aka kammala gasar cikin kwanciyar hankali ya kuma yabawa jami’an tsaron Sojojin Najeriya, kan irin kokarin da suke yi domin kare martabar kasarsu. Yace daga yanzu dajin Sambisa zai kasance wajen da ake baiwa jami’an tsaron Sojojin Najeriya horo.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:26 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG