Shugaban riko na wannan asusu da ake kira ITF Mr Dickson Onuoha, shine ne ya bayyana hakan, lokacin da yake yiwa matasan jawabi da kuma alkawarin ci gaba da taimaka musu, don kasancewa masu dogaro da kai. Yace irin wannan shiri na gudana ne a gaba daya fadin kasar, kuma sukan dauki mutane dari biyar biyar ne a kowacce jiha, amma sun dauki matane 1,100 a jihar Borno wadanda suka hada da ‘yan gudun hijira.
A jawabin na shugaban asusun yace wannan kididdiga na nuna irin Niyya da gwamnatin tarayya ta ke da shi, musamman wajen taimakawa wadanda rikicin Boko Haram ya ‘dai ‘dai ta da kuma matasan kasar. shima manajan wannan shiri na ITF dake garin Maiduguri, Mallam Aminu Hassan, yace wannan horo na watanni Uku ne kuma an kayar da sune akan koyon ‘dinki da kiwon kaji da kuma hada kayan shafe shafe wanda ake amfani da shi yau da kullum a gidaje don rage rashin ayyuka tsakanin matasa.
A wata hira da wakilin Muryar Amurka, Haruna Dauda, yayi da wasu matasan da suka wannan horo sun yaba sosai ga horon da suka samu, inda suka shaida masa cewa ko yanzu suka sami kayan aiki zasu iya bude gurin sana’a. matasan dai sun hada maza da mata, ciki harda wasu ‘yan gudun hijira dake zaune a sansanoni daban daban.
Saurari rahotan Haruna Dauda daga Maiduguri.
Your browser doesn’t support HTML5