Wannan na zuwa biyo bayan ziyarar rabon kayan abinci da atamfofi da katifofi da kuma kayan masarufi ga mata masu shayarwa da ta kai jihohin Yobe da Borno, domin bincikar wadannan zarge-zarge. Da take amsa tambayar wakilin Muryar Amurka, Sanusi Adamu, tace sakamakon ganawa daya-da-daya da ta yi da mata mazauna sansanonin lokacin da ta kai ziyarar binciken gani da ido a sansanin Fofure dake jihar Adamawa.
A ganawar da wakilin Muryar Amurka ya yi da wasu daga cikin mata da suka ci gajiyar tallafin, Malama Zainab Dungus ta tabbatar da wannan matsayi na binciken ministan na cewa babu gaskiyar a batun cin zarafi ko gallazawa mata da yara mata da aka ce ana yi a sansaninsu. Yayin da su kuma Maryam Ali da Fanta Mohammed da bata jima da samu da na miji a sansanin ba ta yaba da tagomashi da suka samu daga shugaban kasa Muhammadu Buhari ta hannun ministan.
Saurari cikakken rahotan Sanusi Adamu.