Rahotanni daga yankin Suleja sun nuna cewa jami’an tsaro suka yi ta harbin bindiga ga masu zanga-zangar a cikin garin na Suleja da kuma wadanda ke kan hanyar Kaduna Road dake kan kokarin zuwa Abuja da Kaduna.
Wani shugaban al’umma a yankin na Suleja da ya bukaci a sakaya sunanshi ya ce mutane uku ne jami’an tsaron suka harbe a cikin garin Suleja yayin da kuma a Kaduna Road mutane biyar.
A karamar hukumar Tafa kuma masu zanga-zangar sun auka sakatariya karama tare da lalata kayan dake ciki inda Barista Musa Kallamu daga yankin ya ce hatta na’urorin kwanfuta na sashen na tara kudaden haraji a karamar hukumar duk an tarwatsasu.
Tunda farko dai wasu daga cikin masu zanga-zangar sun ce suna cikin tsananin tsadar rayuwa saboda haka babu ja da baya sai gwamnati ta dawo da tallafin mai cikin hanzari.
Gwamnatin jihar Neja dai ta ce ta na godiya ga al’ummar jihar da ba su fito zanga-zangar ba a inda aka samu matsalolin kuma suna ci gaba da baiwa jama’a hakuri ne.
Kwamishiniyar Labarai ta jihar Nejan Hon. Binta Mamman ta tabbatar da mutuwar mutane a yankin na Suleja sai dai ta ce ya zuwa lokacin da Muryar Amurka ke magana da ita mutane biyu ne suka tabbatar da mutuwarsu a hukumance.
Kawo lokacin hada wannan rahoto bamu samu wani bayani ba daga rundunar ‘yan sanda ta jihar Neja ba, domin kuwa ko kokarin samun kakakin ‘yan sandan jihar Wasiu Abiodun ta wayar Salulu ya ci tura.
Saurari cikakken rahoto daga Mustapha Nasiru Batsari:
Your browser doesn’t support HTML5