An hallaka wani dan jarida mai daukar hoto wa kafar yada labaran gwamnati a arewacin Nijeriya

  • Ibrahim Garba

Wuraren cinakayya na Manyan biranen Nijeriya kan cunkushe da jama'a idan ana cikin kwanciyar hankali

Wasu ‘yan bindiga sun hallaka wani dan jarida mai aiki da kafar

Wasu ‘yan bindiga sun hallaka wani dan jarida mai aiki da kafar yada labaran gwamnati a wani birnin arewacin Nijeriya, inda wasu masu tsattsauran ra’ayin Islam su ka yi ta kai munanan hare-hare a baya.

Hukumomi sun fadi jiya Lahadi cewa Zakari Isa, wanda ma’aikaci ne na Gidan Talabijin din gwamnatin Nijeriya, ya mutu a birnin Maiduguri bayan da aka bindige shi da daddare. An kai masa harin ne jim kadan bayan ya fito daga masallaci.

Baba wanda ya dau alhakin kai harin nan da nan. To saidai hukumomi na zargin kungiyar Boko Haram, wadda tad au alhakin kai wasu jerin hare-haren bama-bamai da kuma yin kwantan bauna a arewacin Nijeriya, da kuma kai harin bam kan hedikwatan MDD da ke birnin Abuja, inda mutane 23 su ka hallaka.

A watan jiya wannan kungiyar ta yi baranar za ta kai hari kan duk wani dan jaridan day a yada labaran dab a na gaskiya ba ne game das u.

Har yanzu dai ba a san musabbabin wannan kisan ba. Kungiyar ‘Yan Jarida Ta Nijeriya t ace babu wani abu cikin rahotannin Isa das u ka cancanci wannan kungiyar ta auna shi.