Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Gaske Ne Sojojin Ethiopia Su Na Kasar Somaliya


Sojojin kasar Ethiopia
Sojojin kasar Ethiopia

Mazauna yankin tsakiyar kasar Somaliya sun gayawa 'yan jarida cewa sun ga kwambar motocin sojojin Ethiopia na shiga kasar a ranakun Asabar da Lahadi

Ministan tsaron kasar Somaliya ya tabbatar da cewa sojojin kasar Ethiopia su na Somaliya su na yaki da 'yan gwagwarmayar Islama na kungiyar al-Shabab.

Hussein Arab Issa ya shaidawa sashen Somali na Muryar Amurka a jiya Lahadi cewa gwamnati na yin lale marhabun da duk wanda zai taimaka a yaki kungiyar mai alaka da al-Qaida. Ya ce sojojin Ethiopiar za su musanya bayanan leken asiri sannan kuma su yi aiki tare da dakarun gwamnatin kasar Somaliya.

Mazauna yankin tsakiyar kasar Somaliya sun gayawa 'yan jarida cewa sun ga kwambar motocin sojojin Ethiopia na shiga kasar a ranakun Asabar da Lahadi.

Ethiopia ta musanta cewa ta tura sojojinta tsallaken kan iyaka.

A watan jiya Kenya ma ta tura sojojinta zuwa cikin kasar Somaliya su yaki al-Shabab. Kenya ta zargi mayakan na al-Shabab da tsallaka kan iyaka daga Somaliya su na shiga Kenya su na sace 'yan kasashen waje.

Wani sojan kasar Kenya na gadin wani dan karamin filin jirgin sama a wani yankin da ke daf da kan iyakar Somaliya da Kenya inda mayakan al-Shabab suke da karfi
Wani sojan kasar Kenya na gadin wani dan karamin filin jirgin sama a wani yankin da ke daf da kan iyakar Somaliya da Kenya inda mayakan al-Shabab suke da karfi

Tun shekarar dubu biyu da takwas al-Shabab ke fafata yakin neman hambare gwamnatin kasar Somaliya mai rauni. A kwanan baya kungiyar ta fice daga Mogadishu babban birnin kasar, amma har yanzu ita ke iko da wasu manyan sassan kasar ta Somaliya a yankunan tsakiya da kuma kudanci.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG