Jami’in ya kara da cewa jami’an ‘yan sandan sun sami rahotannin cewa wasu mutane ne suka shiga wani kauye da ake kira Kufayi, dake cikin Billiri, kuma rahotannin sun nuna cewa mutanen sun fito ne daga kauyukan dake bangaren Shangwam, amma kawo yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike akan lamarin domin hatta kwamishinan ‘yan sanda yaje wannan waje.
Ya ci gaba da cewa yanzu haka akwai tawaga mai karfi da gwamnan jihar ya kafa wadda ke da jagorancin kwamishinan ‘yan sandan jihar domin su cigaba da sasanta jama’ar yankin baki daya.
A zuwa lokacin da wakilin sashen Hausa Abdulwahab Muhammad ya hada mana wannan rahoto,mai Magana da yawun ‘yan sandan ya bayyana cewa an sami rasuwar mutum guda wani mai suna Inde, mai gadi a wata makarantar horas da limaman kiristoci dake wurin, inad suka far masa har ya rasa ransa.
DSP Ahmad ya bayyana cewa baya ga wannan, babu wani rahoton da ya bayyana wani abu makamancin wannan domin a cewarsa, suna yankin har faduwar rana domin tabbatar da duk abubuwan da suka kasance.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar ya tura rundunar tsaro ta mobile police domin tabbatar da maido da doka da oda a cikin garin.
Ga cikakken rahoton Abdulwahab Muhammad.
Your browser doesn’t support HTML5