Akwai sansanonin 'yan gudun hijira a wurare daban daban cikin jihar kuma wasunsu suna cikin mawuyacin hali saboda ukubar da suka sha ta yunwa a hannun 'yan Boko Haram.
A 'yan makonnin nan kafafen yada labarai da dama suka dinga bada labarin mutuwar yara kanana a wasu sansanonin 'yan gudun hijira sakamakon karancin abinci musamman a wasu sansanonin dake wasu kananan hukumomi. Labaran sun ja hankulan kungiyoyi da gwamnatocin duniya da dama. da gwamnatin jihar Borno da na tarayyar Najeriya.
Hukumar NEMA ta mika kayan abincin ne ga mataimakin gwamnan jihar Alhaji Usman Mamman Durkuwa. Kayan abincin sun hada da buhuhunan shinkafa da na gyero da garin birabisko da kuma wasu kayan abinci masu gina jiki.
Alhaji Usman Durkuwa ya nuna farin ciki da kokarin gwamnatin tarayya tare da mika godiyar gwamnatin jihar ga ita hukumar NEMA..
Alhaji Muhammad Kanar shugaban hukumar a shiyar arewa maso gabas yace hakki ne daga gwamnatin tarayya ta samar wa 'yan gudun hijirar kayan abincin da za'a dafa ita kuma gwamnatin jiha ta bada kayan hadawa. Kawo yanzu suna da sansanoni 16 cikin birnin Maiduguri.
Kayan abincin da NEMA ta bayar yanzu zai kai wata daya kafin ya kare. Nufin hukumar shi ne ta dinga bada kayan abincin kowane wata .
Yaran da rashin abinci ya addabesu wadanda sojoji suka kwato ne daga hannun 'yan Boko Haram. Yayinda suke hannun 'yan ta'adan da kyar suke samun abinci sau daya cikin ranaku biyu ko uku domin sai abun da dan Boko Haram ya kawo ya basu. Yace da farko sun dauko mutane 1800 da suka hada da mara lafiya.
Injiniya Ahmed Satomi shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Borno ya yi karin bayani. Yace suna da sansanin 'yan gudun hijira wajen 12 a wajen Maiduguri. Akwai kuma wasu a tsakiyar jihar a Bama da mutane 25,000. Ya lissafa garuruwan da suke da sansanoni.
Gano irin halin da 'yan gudun hijiran suke ciki ya sa gwamnatin tarayya ta bada umurnin a dinga sayen abinci ana rabawa.
Ga karin bayani.