Cibiyar Center for World University Ranking dake lura da lamuran jami'o'i a duk fadin duniya ta fitar da rahotonta na shekarar 2016 wanda ya nuna cewa har yanzu babu wata jami'a a Najeriya da ta samu shiga cikin jami'oi 1000 mafi inganci a duniya.
Rahoton ya nuna jami'o'in Harvard da Stanford dukansu a Amurka su ne suka zo na daya da na biyu a duniya. Haka ma ta ukun ta Amurka ce , wato MIT dake Boston.
A can Birtaniya kuma akwai jami'o'in Cambridge da Oxford da suka zo na hudu da na biyar.
Nahiyar Afirka ma ba'a barta a baya ba. Wasu jami'o'in Afirka ta Kudu da Masar suka samu shiga jerin sunayen jami'o'i 1000 da ake ji dasu a duniya. Daga Afirka ta Kudu jami'o'i biyar ne suka samu shga yayinda guda hudu suka shiga a kasar Masar.
Muryar Amurka ta tambayi wani Malam Muhammad Sani na jami'ar jihar Kaduna akan dalilin da ya sa jami'o'in Najeriya basa samun shiga wannan rukuni na jami'o'i mafi inganci a duniya.
Yace hukumar dake kula da jami'o'i a Najeriya ko NUC bata da nata ma'aikatan din din din da zasu yi aikin. Sau tari idan zata binciki jami'o'i sai ta je wasu jami'o'in ta dauko mutanen da zasu yi aikin na wucin gadi. Tana yiwuwa malaman da ta dauko suna koyaswa a jami'ar da aka turasu su bincika. Babu yadda irin wadannan malaman zasu rutuba a cikin rahotonsu cewa jami'o'in da suka bincika basu da kayan aiki ko basu cancanta su bada wani digiri ba.
Daliban jami'o'in Najeriya sun nuna takaicinsu a kan rahoton, suna cewa ke nan idan sun gama a Najeriya suka fita waje karo ilimi ba za'a amince da digiri dinsu ba ko kuma a hanasu aiki. Sun kira gwamnati ta tashi tsaye ta taimaka wajen inganta harkokin koyaswa a jami'o'in kasar.
Ga karin bayani.