Ministan shari’a Abubakar Malami yaki amsa tambayoyin da wakiliyar sashen Hausa na muryar Amurka Madina Dauda, ta yi masa, ta dalilin haka ne ta nemi jin ta bakin daya daga cikin ‘ya’yan kwamitin dake kula da shari’ar Joshua Lidani, ko sun gamsu da amsar da malami ya basu?
Sai ya amsa yace “A’a bamu gamsu ba, domin bayanin da yayi ya nuna cewa maganar na kotu saboda haka bazai yi wani bayani ba. Mukuma dalilin dayasa muka kira shi shine bamu hana zuwa kotu ba idan mutum ya aikata laifi, abinda muke bukata kawai shine a bi matakan da suka dace kafin aje kotu, domin akwai tabbatattun shaidu, domin wadannan mutane shugabanni ne a majalisa”.
A tambayar da Madina Dauda ta sake yi masa, cewar wasu na ganin cewa kamar ministan shari’ar ya fi gaskiya a cikin lamarin, kuma idan suna da gaskiya su bari a kammala shari’ar, mai yasa suke shiga harkar? sai Mr Joshua Lidani ya kada baki yace
“Ba muna shiga harkar bane, muna kokari muga cewar an bi ka’ida ne a cikin lamarin, domin haka duk abin da za’a yi tunda shugabanni ne a majalisa ya kamata a tabbatar anbi doka”
Tun a makon daya gabata ne ministan ya ki bayyana a gaban kwamitin shari’ar har sau biyu, matakin da ya harzuka majalisar dattawa inda tayi barazanar yin amfani da karfin ikon da tsarin mulki ya tanadar mata na bada umurnin cafko ministan.
Ga cikakken rahoton Madina Dauda