Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Kwastam Ta Yi Babban Kamu Harda Mota Mai Sulke


Hukumar kwastam ta Najeriya mai kula da jahohin Oyo da Osun ta cafke wasu manyan motoci makare da buhuhuwan shinkafa, da jarkokin man girki, da tayoyin mota, da tufafin gwanjo da motocin kasaita Jeep ciki harda mai sulke wadda harsashi baya hudawa, da sauran kayayyaki da aka kiyasta kudin su yakai daruruwan miliyoyin Naira.

Hukumar ta kwastam ta tara biliyoyin kudin shiga a cikin watanni shidda na wannan shekarar. Babban jami’in hukumar mai kula da jihohin Oyo da Osun Mr Ogunkowa TBM ne ya jagoranci taron manema labarai wadanda suka je shalkwatar kwastam a Ibadan domin ganewa idanun su abubuwan da aka kama.

Mr Ogunkowa TBM yace “zamu nuna maku kayayyakin da muka kama cikin makonni uku, ciki harda wata motar kasaita samfarin Jeep Toyota Prado mai sulke mai launin baki wadda harsashi baya fasawa, da manyan motoci shake da buhuhuwan shinkafa lalatatta, da motoci kanana da manya da aka shigo dasu Najeriya ta bayan gida, da abubuwa da dama.

Bayan nunawa ‘yan jarida abubuwanda jami’an suka kama, babban jami’in ya fadawa manema labarai irin kudaden da suka tara na shiga a cikin rabin shekara wato Naira bilyan bakwai da miliyan dari biyu da arba’in da biyar, da dubu dari shidda da tamanin da dari biyar da tamanin da bakwai da kwabo sittin da tara.

Shugaban yayi kira ga jama’a dasu ba hukuma goyon baya da hadin kai wajan tona duk wani abu da ake shigowa dashi kasar ba bisa ka’ida ba.

Ga rahoton Hassan Ummaru Tambuwal.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG