An Hallaka Fitaccen Dan Jarida A Ukraine

A jiya Laraba ne aka kashe wani fitaccen ‘dan jarida a wata fashewar mota a Kyiv babban birnin Ukraine.

Kafar watsa labaran gwamnati ta fitar da rahotan dake cewa, Pavel Sheremet, wakilin babban gidan jaridar Ukrainska Pravda wadda ke kan yanar gizo, ya rasa ransa a lokacin da wani abu ya fashe a motar yayin da yake kan hanyarsa zuwa wajen aiki. Hotunan sun nuna yadda motar ta kone kurmus baki daya kofofin motar hudu a bude.

Shugaban ‘yan sandan Ukraine, Khatia Dekanoidze, yace ana bincikar fashewar a matsayin kisan gilla, kuma an saka bom a motar wanda yakai nauyin gram 400 zuwa 600.

Sheremet dai ‘dan jarida ne mai ra’ayin Yamma wanda aka haifa a Belarus, amma ‘dan kasar Rasha ne, kashe shi da akayi ya girgiza kasar Ukraine da ‘yan Jarida baki ‘daya.

A nan Washington, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka, John Kirby, yace Sheremet “ya taka muhimmiyar rawa a dimokaradiyar Ukraine.” Ta hanyar yin rahotanni akan batutuwa da suka hada da cin hanci da rashawa da kuma ayyukan gwamnati.