Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Yau Ake Bude Babban Taron Jam'iyyar Republican


Nan da zuwa karshen makon nan ne ake sa ran jam’iyyar Republican za ta tsayar da Donald Trump a matsayin dan takararta a hukumance, lamarin da zai baiwa masu kada kuri’a a Amurka damar yin zaben shugaban kasa a ranar 8 ga watan Nuwamba.

A yau Litinin aka bude babban taron Jam'iyyar Republican a birnin Cleveland da ke jihar Ohio inda taron zai fi maida hankali kan batutuwan tsaron kasa da baki.

Daga cikin wadanda za su yi jawabi akwai tsohon gwamnan jihar Texas, Rick Perry, da mahaifiyar wani Ba’amurke da aka kashe a Benghazi da ke Libya, da masu fafutukar neman a samar da sauye-sauye a fannin shige da fice a kasar, da tsohon Magajin Garin New York, Rudy Guiliani da kuma uwargidan Trump Melania.

A wata hira da gidan talbijin na CBS ya nuna mai taken 60 Minutes a ranar Lahadi, Trump ya amsa wata tambaya kan halin da duniya ke ciki, wacce ake ganin somin-tabi ce dangane da irin caccakar da shugaba Barack Oabma da ‘yar takarar Democrat Hillary Clinton za su sha a wannan mako.

A baya, Trump ya ba da shawarar gina wata Katanga a kan iyakar Amurka da Mexico da kuma hana musulmi shiga kasar, koda ya ke a hirar ta jiya Lahadi, ya dan sassauta matsayarsa kan hana musulmi shiga Amurka, inda ya ce a fi maida hankali kan kasashen da mutane suka fito.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG