An Gurfanar da Dillalan Makamai Gaban Shari'a a Nigeria
Jami’an Nigeria ne suka kame tulin makama a tashar jiragen ruwan Apapa dake birnin Ikon, kuma an kwaso makaman ne daga tashar jiragen ruwan Iran ta Banadar Abbas, aka rubuta cewar kayan gini ne. Lauyan wadanda ake yiwa shari’a Lauya Uche yana mai cewa babu wata niyya ta yin amfani ko ajiye wadannan makamai a Nigeria. Takardun shigada fitar da kaya daga jirgin ruwa sun tabbatar da cewar makaman suna kan hanyarsu ce ta zuwa kasar Gambiya, za’a kuma gabatarwa kotun da dukkan takardun da suka jibanci kaiwa da komowar wadannan makamai. Nigeria ta gabatar da kukanta gaban kwamatin sulhun MDD tana zargin kokarin da Iran keyi domin yin watsi da takunkumin da MDD ta azawa mata.Gwamnatin kasar Gambia tace ba abinda ya hadata da batun cinikayyar makamai da kasar Iran harma Gwamnatin Gambia ta katse huldar jakadanci da kasar Iran.