Hukumomi sun ce mafasan teku da dama dauke da bindigogi sun kai hari kan wani jirgin dakon sinadarai a kusa da gabar Nijeriya
Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen ruwa ta kasa da kasa tace al’amarin ya faru ne jiya Alhamis a mashigar ruwan Guinea, mai nisan kilomita 80 daga birnin Lagos.
Hukumar t ace mafasan sun bude wuta kan jirgin ruwan sannan su ka yi kokarin hawa ciki, to amman bayan sun yi ta fama na awoyi sais u ka daina bin jirgin.
A wani al’amarin kuma irin wannan, jami’an kula da zirga-zirgar jiragen Girka sun ce mafasan tekun Nijeriya sun sako manyan sojojin ruwan girka biyu da su ka kama daga cikin wani jirgin dakon kayan Girka a watan jiya.
A wannan harin, wasu ‘yan bindiga dadin Nijeriya sun hau cikin jirgin su ka su ka kama jami’an biyu – wato da Kaftin din jirgin dan asalin Ukrain da kuma Injiniyan jirgin dan asalin Girka. Maharan sun kuma raunata wasu ma’aikatan jirgin su biyu.
Wannan harin kuma ya auku ne a kusa da Tashar Jirgin Ruwan Nijeriya da ke Onne, a yankin Kudancin kasar mai arzikin man fetur na Niger-Delter.