An Gurfanar Da Wasu Matasa Biyu 'Yan Uwan Juna Da Suka Saci Kaji

An gurfanar da wasu matasa biyu ‘yan uwan juna masu shekaru 35, da 25, a wata kotun majististire dake jihar Ondo a sakamakon kama su da aikata laifin satar kaji a lokacin kirsimeti da aka kiyasta kudin su zasu kai dubu ashirin da biyar.

Mujallar Daily Trust, ta wallafa cewa kotu ta caji matasan biyu da mai sana’ar aski da kuma birkila, basu da wani takamaiman adireshi da laifuka uku, wato hada kai, da zamba da kuma sata.

Dan sanda mai gabatar da kara mai mukamin saja, Ayodeji Omoyeigha, ya fadawa kotu cewar ranar 23, ga watan Disambar shekarar data gabata ne matasan ‘yan uwan juna suka hada baki wajan satar kajin mutane.

Ya kara da cewa matashi na farko ya saci kaji guda uku na wani Olabisi Mathew, da suke kulle a keji da kudin su ya kai kudi Naira dubu goma sha biyar. gudan kuma ya saci guda biyu ne suma kulle a kejin wani mai suna Mayowa Taiwo, kuma kudin su zasu kama Naira dubu goma.

Mai shari’ar ya ce matasan da ake tuhuma sun aikata laifin da ya sabawa doka a karkashin sashi na 516, 412 da 390 (9) na dokokin jihar Ondo.

Alkalin kotun ya bada belin matasan akan kudi Naira dubu Talatin, da kuma bukatar su mika takardun su shaidar biyan haraji na shekara, kana ya dage sauraren karar zuwa ranar 2 ga watan Fabarairu.