NIAMEY, NIGER - Kungiyoyin kare hakkokin yara a Nijer sun jaddada aniyar sake jan damara don fadakar da jama’a illolin da ke tattare da wannan al’amari, a cewar Bachar Maman shugaban gamayyar kungiyoyin Esperance a hirarsu da Muryar Amurka.
Maman ya ce wani binciken kungiyar FAO ya nuna cewa wannan matsala ta aikin yara akwai ta a Nijer a fannin noman shinkafa a jihar Yamai, Tilabery, da Dosso. Yara kan taba takin zamani da magungunan kwari da hannuwansu ba tare da sanin illolin da ke tattare da hakan ba.
A Maradi kuwa iyaye kan dora wa yara kanana talla, abinda ka iya jefa su cikin hadari idan suka hadu da miyagun mutane, sannan a jihar Tahoua akan ga yara ‘yan shekara 9 a kan titi suna shaye shaye da karuwanci da dare kuma akwai iyayen da ke boye suna tura su domin su samu abinda zasu yi rayuwa, a cewar Maman.
Ya kara da cewa bara ita ma wata matsala ce a kasar inda ake amfani da yara. Sai ka ga mutun daya dauke da yara uku suna bara domin su kawo masa kudi, har ma hayar yara ake badawa domin su yi bara.
A saboda haka, a cewar Maman, aiki na farko da suka fi maida hankali a kansa shi ne wayar da kan masu kamfanoni da sauransu domin su kiyaye doka wajen daukar yaran da shekarunsu ba su kai na aiki ba.
Saurari cikakkiyar hirar da Souley Moumouni Barma ya yi:
Your browser doesn’t support HTML5