AGADAS, NIGER - A ‘yan shekarun nan dai hukumomin kiwon lafiya sun tashi haikan dan ganin cewa sun murkushe cutar bayan samun muatne 16 da suka kamu da ita.
Rabuka Ali jami’I a ma’aikatar kiwon lafiya a Agadas ya ce babbar matsalar da ake fuskanta wajen yaki da wannan cutar itace rashin samun amincewar wasu iyayen yara wajen yiwa yaransu rigakafin.
Wasu kuma daga cikin iyayen sun amince da ayiwa yaransu rigakafin na polio. Amma yanzu haka dai akwai mutane da dama dake rayuwa da wannan cutar a Nijar.
To sai dai hukumomin kiwon lafiya a Nijar na ci gaba da wayar wa da iyaye kai domin su fahimci anfanin wannan rigakafin ta fannin tabbatar da tsabta acikin al’umma ta la’akari da cewa rashin tsabta na taimakawa wajen yaduwar wannan cutar.
Saurari rahoto cikin sauti daga Hamidan Mahmud: