Daruruwan mutane ne suka hallara a cibiyar kula da tattara gudunmowar jini CNTS ta babbar asibitin Yamai domin halartar wannan gangami dake hangen ankarar da jama’a fa’idar bada jini a albarkacin ranar masu bada jinita duniya.
Ministan kiwon lafiyar al’umar Dr Iliassou Idi Mainassara ya bayyana mahimmancin wannan rana inda ya ce rana ce da kowa ya kamata karrama.
Uwargidan shugaban kasar Nijar Hajiya Hadiza Mohamed Bazoum wacce ta jagoranci wannan biki ta yi kiran jama’a su maida hankali akan wannan aiki na ceton rayuwa wanda ta ce cike yake da dumbin lada.
Wasu daga cikin mahalartan bikin da suka amsa kiran na mahukunta, Adjudant Chef Saidou Abdourahamane Diallo hafsan soja ya je ya bada jini.
Hukumar lafiya ta duniya OMS ta bayyana cewa yawan masu bada jini ya karu a ‘yan shekarun nan a Nijar daga mutun 158,000 a shekara zuwa 168,000 lamarin da ya sa mahukuntan kasar bullo da matakin karfafa gwiwa ga irin wadanan mutane ta hanyar ba su lambobin yabo.
Hamidou Boulhassane Anza wanda ya shafe shekaru 42 yana bada jini na daga cikin wadanda aka karrama.
A albarkacin zagayowar wannan rana Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci gwamnatocin kasashe su karfafa ayyukan waye kan al’uma a game da mahimmancin bada jini a kai-akai don raya duniya ta hanyar tanadin jinin da zai wadaci bukatun marasa laliya.
Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5