An Gano Wasu Sawun Dinasaur Masu Shekaru Sama Da Milliyan 170

An gano sawun takon kafafun dabbar “Dinosaurs” da aka kiyasta shekarun su da suka kai kimanin shekaru milliyan dari da saba’in 170.

Manazarta a karon farko sun gano sawayenne a wani tsibiri a kasar Scotland, wanda hakan ya bayyana cewar dabbobin sunyi rayuwa a shekaru da dama da suka gabata.

A cewar shugaban binciken Dr. Steve Brusatte, na jami’ar Edinburgh “A duk lokacin da suka zurfafa bincike a tsibirin, sai an gano wasu karin sawayen dabbar Dinosaur, da suka kwashe shekaru da dama”.

Sababbin sawayen da aka gano sun bayyana alamun launukan dabbar Dinosaur, kala biyu, daya daga ciki na da wuya mai tsawo, kana dayan kuwa na da hakora masu kaifi.

Yankin na da matukar muhimanci wajen binciken wasu halittu da suka rayu a yankin kuma suka gabata, ganin cewar abubuwan da aka gano a yankin ba kasafai ake ganin suba.

Sahun dabbar dainaso nada wuyar nazari, wanda aka yi amfani da nau’rar jirgi mai tuka kansa “Drone” wajen daukar hotuna da daukar hoton taswirar yankin baki daya.