Mun daina sharhin fina-finan Hausa na Kannywood sakamakon wasu dalilai, a kan haka ne muke yin kokarin fito da wata sabuwar manhaja wadda za a rika koyar da fim ta yadda idan an fitar da shi mutane daga sassan duniya da dama zasu yarda da ingancin sa, inji shugaban jami’ra karatu daga gida wato NOUN, farfesa Abdallah Uba Adamu.
Farfesa Abdallah, ya ce, sun daina sharhi ga fina-finai don haka sabuwar manhajar koyar da fim zata kawar da kurakuran da akan samu a fina-finan Hausa da basu kamata ana samu a fina-finan ba, haka kuma zai dawo da martabar fina-finan Hausa.
Farfesa ya kara da cewa wannan sabon kwas zai maida hankali kan matasa masu tasowa, kai hatta ma wadanda suka dade a masana’antar shirya fina-finai na iya neman gurbin karatu domin inganta sana’arsu da zarar sun fuskanci bukatar yin hakan.
Farfesa Abdallah, ya ce babu wata masana’antar shirya fina-finai da za a ce karfinta ya kai kima, a kowane lokaci masana’antar shirya fina-finai tana kan hanyar bin sahun manyan masanaantu na duniya.
Daga karshe ya kara da cewa abinda ya sa suka kirkiro wannan sabuwar manhajar shine domin ba fina-finan Hausa daraja da zata nuna asalin da al’adar Hausa sabanin yadda ake yi a yanzu a wasu fina-finan.
Facebook Forum