Na fuskancin kalubale daga bangaren dangi na a lokacin da na fara waka sakamakon suna tunani harkar waka harka ce ta lalacewa da bata tarbiya, sai da na shafe tsawon lokaci kafin su farga inji mawaki Ismail Yusuf wanda aka fi sani da Baffan Suri.
Matashin ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilyar DandalinVOA inda ya ce yau da gobe da yawan sanya wa iyayensa wakokin da yake rerawa domin su saurari kalaman da yake fitarwa ne ya sa suka fara gane cewar waka wata hanya ce ta fadakarwa a wannan lokaci ne suka fara mara masa baya.
Baffan Suri, dai mawakin nananye ne ya ce ya fara waka ne sakamakon sha’awa da sanadiyar budurwara wacce aka hana su soyayya sakamakon iyayen ta sun hana.
Ya kara da cewa sanadiyar hakance ta sa ya rera waka domin huce takaicin hana soyayyar da aka yi, kuma ta hakan ne ya isar da sako ga iyaye ko masu hana soyayya tsakanin mutane biyu.
Baffan suri, ya ce ya fi yin wakar soyayya domin ya fadakar ya kuma ilmantar tsakanin al’umma.
Facebook Forum