Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Destiny Peter: Mata A Sauya Tunani Wajan Neman Sana'ar Hannu


Sabulun Gargajiya
Sabulun Gargajiya

Ganin yadda matasa da suka kammala karatun jami’a ke shafe shekaru da dama suna neman aiki ya sa na sauya tunani na tare da samawa kai na sana’ar hannu domin dogaro da kai ko da bayan kammala karatun ba zan sha wahalar neman aiki ba inji matashiya Destiny Peter.

Ta ce tana sana’arta ne a lokutan da bata zuwa makaranta, a cewarta tana jami’ar Bayero ta Kano inda ta ke mataki na uku na karantun jami’a.

Destiny ta ce tana sana’ar gyaran jiki ne ga mata inda bayan ta samu lalura ta fata ta je wata makaranta aka koya mata yadda zata kare fatar ta daga kamuwa da wasu cututtuka ta hanyar hada sabulun wanka.

Ta kara da cewa tana duba fatar mace kafin ta hada mata sabulun da zai dace da ita kuma ta shafe kimanin shekaru uku tana wannan sana’a. Destiny ta kara da cewa ta samu alfanu da dama domin da wannan sana’a ta ke yi wa kanta hidima ta karatu da yau da kullum ba ya ga taimakawa jama’a da ta ke yi.

Daga karshe ta ja hankalin mata da su sauya tunanin su wajen neman sana’ar hannu domin zama masu dogaro da kai gudun kada a zama zauna gari banza sa’annnan a zamewa iyaye ko wadanda ake zaune a wajensu nauyi na yau da gobe.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:35 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG