WASHINGTON, DC —
Hukumomin kasar Kamaru, sun fara maido da ‘yan Najeriya, kusan dubu goma sha biyu, dake gudun hijira a kasar.
Hukumar bada agajin gaggawa na jihar Adamawa, ne suka tarbi ‘yan gudun hijira bayan da jami’an tsaro suka tantance su.
Da yake bayani kan ‘yan Najeriya, dake komowa gida, shugaban hukumar bada agaji na jihar ta Adamawa, Alhaji Haruna Hamaboro, yace hukumarsa ta samu takarda daga hukumomin kasar Kamaru cewa zasu maido da ‘yan gudun hijira dubu goma sha biyu dake kasar ta Kamaru.
Shi kuwa babban jami’in hukumar bada agajin gaggawa ta kasa wato NEMA, mai kula da sansanonin ‘yan gudun hijira dake jihar Adamawa, Alhaji Sa’adu Bello, yace akasarin wadanda suka dawo suna cikin koshin lafiya,