Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Shirin Inganta Tsaro Dan Ta'addanci


Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya

Gwamnatin jihar Adamawa, ta yanke shawarar sanya Sarakunan gargajiya da shuwagabanin al’uma, a sabon shirin inganta tsaro da tada komadar masu karamin karfi.

Wannan ya biyo bayan ganin cewa jihar na cikin jihohin dake fama da matsalar tsaro masamman ta fuskar hare haren ‘yan Boko Haram, da masu sace mutane suna neman kudin fansa.

Gwamnan jihar Muhammadu Bindowa Jibirila, ne ya furta haka a lokaci da Sarakuna suka kai masa ziyara a gidan Gwamnati a Yola, yace, “Idan muka rike Sarakunan gargajiya wadannan matsalolin da aka samu na ta’addanci da bai kai haka ba, domin bakin da suke shiga gari ba’a gane su, toh ida ace an baiwa sarakuna martabar da yakamata babu wani mutun da zai zo ko sarkin tasha yasan bako.”

A kwai kudaden da aka tanada domin wannan sabon tsari, yayin da aka baiwa masu unguwani, Hakimai dama Dagatai ikon kamawa da kuma korar duk wanda basu amince da shi ba a cikin al’uma dan mikawa ga jami’an tsaro.

Mai martaba Lamidon Adamawa, Dr. Muhammadu Barkindo Aliyu Mustapha, shugaban majalisar Sarakunan jihar yace Sarakunan jihar zasu hada kai da Gwamnatin jihar domin samun nasarar aiwatar da duk shirye shiryen Gwamnati.

XS
SM
MD
LG