An Fara Gardama Akan Kisan Zamfara

Mutanen da aka kasha a jihar Zamfara, lokacin da ake yi musu jana'iza, 6 ga Afirailu 2014.

​Sanata Sa’idu Dansadau daga jihar Zamfara yayi tsokaci akan kisan gillar da akayi a jihar, kwanakin baya.
Sanata Dansadau yace “kawai suka zo, suka kama harbin mutane. Abunda ya tayar mana da hankali shine, a madadin hukuma ta tausaya mana, an ce a’a, wai muke da laifi.”

Amma komishinan ‘yan sandan jihar, Ibrahim Birnin Magaji ba haka yake ganin lamarin ba “su kansu, gwamnoni na wadannan jihohi, Kaduna da Neja, da Kebbi, suma Sa’idu Dansadau yaci amanarsu domin mutanensu ne ya dauko aka zo, aka yi wannan taro, ba tare da sanin hukuma ba.”

Hukumomin Jihar Zamfara sun ce mutane 119 ne aka kashe a lokacin da wasu 'yan bindiga a kan babura suka kai farmaki kan Unguwar Galadima dake karamar hukumar Maru mako daya da ya wuce.

Mutanen garin sun ce wadanda aka kashe sun fi mutane 150. Wakilinmu Murtala Faruk Sanyinna yace ya kirga gawarwaki 92 a wurin da aka hallara domin yi musu jana'iza.

Yanzu haka ana ta nuna yatsa akan menene ya jawo lamarin, da kuma ko wanene yake da laifi.