Janaral Mansur Dan Ali mai ritaya daya daga cikin wakilan dake halartar taron kasa daga jihar Zamfara, yace babu abun da ya sa gaba sai zaman lafiyar Najeriya da cigabanta. Yayin da yake zantawa da manema labarai Janaral Ali yace ashirye yake ya tsawatawa duk wadanda suke son su kawo wani abun da ya sabawa kasancewar Najeriya zama kasa daya ko kuma rabuwar kan 'yan Najeriya. Yace tun asali ya bayarda rayuwarsa ga aikin soja yanzu kuma ga taron kasa inda za'a tattauna kan yadda kasar zata cigaba. Yace da yadda Allah za'a sami cigaba domin shugaban kasa ya fada cewa za'a tattauna komi amma banda batun Najeriya a matsayinta na zama kasa daya.
A taron kasa maganar raba kasar bata ciki. Yace kodayake shi ba dan siyasa ba ne amma a kishin kasa babu wanda ya fi shi. Koda wasu sun yi shiri da zuwan su zo su raba kasar zasu kwance wannan shirin.
Mai sharhi kan alamuran yau da kullum Bashir Baba na ganin bude taron da Pastor Tunde Bakare yayi da addu'a ba laifi ba ne ganin cewa Najeriya kasa ce da ta kunshi addinai da yawa. Ya cigaba da cewa wakilai daga sassa daban daban suka riga suka tsara gadawali kamar Yarbawa da Igbo duk sun tanadi kundi. Amma wakilan arewa zasu tafi taron ko takardar tsire babu a hannunsu.
Ga karin bayani.