Ya furta haka ne da yake maida martani ga batun da shugaban kasa Goodluck Jonathan da wasu makarrabansa suka ce wai sakacin gwamnoni ne ya haifar da rashin tsaro a wasu jihohi.
Gwamnar Abdulaziz Yari, yace “kamar yanda muka sani tabbatar da tsaro daga farkon sa har karshen sa babu hannu gwamnatin jihar a ciki.”
Yace domin inda da hannu ta a ciki shine zata iya magana idan anyi dai-dai za kayi hukumci inda bayi dai-dai ba zaka dauki mataki inda aka kasa zaka cika, da ta raba da gwamnatin jihohi kamar yanda aka raba harkan ilimi, samar da ruwa da hanyoyi.
Shima shugaban kasa, yace rashin rikon amana da iya gudanar da mulki a wasu jihohi na Najeriya masamma a arewa na kan gaba akan jerin abubuwan dake kawo matsalolin na tsaro domin rashin aikin yi da samar da ilimi ma inganci,ke haifar da harkoki irin na ‘yan Boko Haram.