An Dage Dokar Hana Fita a Jihar Tarba

Yanzu haka dai hankali ya kwanta a yankunan Taraba, bayan wani hargitsi mai nasaba da sakamakon zaben gwamna a jihar inda aka sami hasarar rayuka da kuma kone-kone a garin Gyambu.

Rahotanni sun nuna cewa bayan garin Gyambu an sami barkewar hatsaniya a wasu sassan jihar ta Taraba musamman a tsakanin magoya bayan dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar wato Architect Darius Ishaku da kuma magoya bayan ‘yar takarar jam’iyyar adawa ta APC sanata Aisha Jummai Alhassan da ake yi wa lakabi da Maman Taraba.

Sakamakon wannan hatsaniyar ne ya sa gwamnatin jihar kafa dokar hana fita tun daga karfe bakwai na maraice har zuwa karfe shida na safe.

ASP Joseph Kwaji ya tabbatar da cewa hankula sun kwanta bayan rigimar da ta kacame tsakanin ‘yan PDP da ‘yan APC ya kuma ce an baza 'yan sanda a yankunan.

‘Yan takarar kujerar gwamna da ‘yan jam’iyyunsu sun maida martani game da takaddamar soke zabe da sake shi a wasu yankuna da ake zargin an sace akwatunan zabe da kuma aringizon kuri’u.

Chief David Sabo Kente, dan takarar jam’iyyar SDP ya ce su kam sun yi na’am da batun sake zaben.

Shi kuma dan takarar jam’iyyar PDP Architech Darius, a ta bakin wani hadiminsa, ya fadi cewa ba a yi masu adalci ba.

A nata bangaren kuma, jam’iyyar adawa ta APC ta bayyana rashin jin dadinta bisa ga matakin da aka dauka a ta bakin shugabanta Malam Jika Ardo.

Inda ya ce duk da cewa hukumar zabe ke da hurumin daukar matakin kuma ba abin da za su yi, abin dai bai yi ma ‘yan jam’iyyar dadi ba saboda tun kafin zabe sun gabatar da koke-kokensu amma ba a saurare su ba.

Ga karin bayani daga Ibrahim Abdul’aziz.

Your browser doesn’t support HTML5

An Dage Dokar Hana Fita a Jihar Tarba - 2'49"