An Cimma Yarjejeniyar Da Ta Kawo Karshen Yajin Aikin Jaruman Hollywood

Hollywood Strikes

Kungiyar jaruman fina-finan Hollywood ta cimma matsaya da kamfanonin hada fina-finai a ranar Laraba don kawo karshen yajin aikin da ta yi, wanda ya kawo kusan watanni na rikicin ma’aikata ya kuma kawo cikas ga masana’antar nishadi a tarihi.

WASHINGTON, D. C. - Dole ne a kada kuri’a don amincewa da yarjejeniyar kwantiragin ta tsawon shekaru uku daga shugabannin kungiyar da mambobinta a cikin kwanaki masu zuwa, amma shugabannin sun bayyana cewa yajin aikin zai kawo karshe da karfe 12:01 na safe ranar Alhamis.

Hollywood Strikes

Fiye da mambobi 60,000 na kungiyar Actors Guild-American Federation of Television and Radio Performers suka shiga yajin aiki tun ranar 14 ga Yuli, tare da marubutan labarai da suka bar aikin fiye da watanni biyu da suka gabata.

Wannan dai shi ne karon farko da kungiyoyin biyu suka fara yajin aiki tare tun daga shekarar 1960. Kamfanonin hada fina-finai sun zabi tattaunawa da marubutan da farko, inda suka cimma yarjejeniyar da shugabancinsu ya nuna a matsayin babbar nasara da kawo karshen yajin aikin a ranar 26 ga Satumba.

Ba a fitar da sharuddan yarjejeniyar ba nan take. Kungiyar SAG-AFTRA ta ce za a ba da cikakkun bayanai bayan wani taro a ranar Juma'a, inda mambobin kwamitin ke duba takardun yarjejeniyar.

Abubuwan da ke kan teburin sun haɗa da biyan wasu kudade na karamın lokaci da kuma biyan kuɗadenayyukan da aka yi na baya na fina-finai da wasan kwaikwayo na talabijin, tare da baiwa jarumai damar kula da hotunansu da kuma amincewar da suka samu hanyar amfani da fasara mai zurfin tunani ta AI.

-AP