A daren yau Lahadi, za a yi bikin karrama fina-finai na Oscars a nan Amurka, inda masu ruwa da tsaki a masana’antar dandalin hada fim na Hollywood, za su hallara a wannan bikin ba da lambar yabo mafi girma a duniyar hada fim.
Fina-finai 9 aka tantance, wadanda za su nemi lambar yabo da ta fi daraja cikin kyaututtukan da za a bayar a rukunai daban-daban – wato lambar yabo ta fim din da ya fi inganci.
"Ni a wurina, bikin karrama fina-finai na Oscars, ya hade wuri guda, wasannin Super Bowl da Olympics da Gasar cin kwallon kafa ta duniya wato World Cup.” Inji Greg Donovan, jakada a dandalin shirya fina-finai na Hollywood.
Jama’a da dama na ganin fim din “World War (I) 1917” shi ne zai lashe babbar kyautar, ko da yake, akwai sauran fina-finai da ke hammaya da shi, irinsu “Parasites” da “Once Upon a Time in Hollywood.”
Bikin, wanda za a yi birnin Los Angeles har ila yau, zai karrama jarumi da jaruma da darektan da suka fi kwarewa.
Sai dai kamar yadda aka gani a shekarun baya, a bana ma, bikin na fuskantar suka kan yadda ya fi samun wakilcin fararen fata fiye da bakake.
Cynthia Erivo, ita ce bakar fata tilo da ta samu shiga rukunin wadanda za su kara a neman kambun jarumar da ta fi kwarewa a wannan shekara.
Amma hankula sun fi karkata kan jaruma Renee Zellweger, a matsayin wacce za ta lashe kyautar.
Bikin na Oscars har ila yau, ana sukar shi da rashin cikakken wakilcin mata idan aka kwatanta da takwarorinsu maza da suka fi karuwa da shi.