Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Tayi Alkawarin Tallafawa Najeriya Ta Fuskar Kirkirekirkire Da Fasahar Zamani


Akunno Cook
Akunno Cook

A karshen wata ziyara ta kwanaki uku da ta kawo Najeriya, mataimakiyar sakatatiyar harkokin wajen Amurka mai kula da nahiyar afrika Madam Akunno Cook ta jaddada kudirin kasar Amurka  na tallafawa Najeriya samun nasara a fannonin kirkire kirkiren fasahar zamani da Finafinai domin cigaban kasa. 

A wata ganawa da ta yi da ministan yada labarai Lai Mohammed, mataimakiyar sakatariyar harkokin wajen na Amurka Miss Akunno Cook tace ta gamsu da kokarin da Najeriya ke yi wajen bunkasa fannonin kirkire kirkiren zamani da kuma bunkasa fannonin finafinai ta anfanin da fasahohin zamani ko "digital technology" a turance.

Akunno ta shedawa ministan yada labaran Najeriya cewar kokarin gargado da dandalin wasannin kwaikwayo na kasa wato Natuonal Theater da ke nan Lagos, abun yabawa ne matuka, ganin yarda harkokin wasannin kwaikwayo ko finafinai ke tattare da dinbin kudaden shiga, kamar dai yarda ake gani a duniyar wasannin kwaikwayo na Hollywood da kuma na wasu kasashen duniya.

Don haka ta jaddada kudin gwamnatin amurka na tallafawa Najeriya ta wannan fuskar domin a gudu tare a tsira tare. Musanman bisa la'akari da muhinmancin su a tsarin demokradiyya ganin nan gaba kasar zata shiga zaben kasa.

A bangaren sa Ministan labarai Lai Mohammed yace Najeriya na matukar bukatar tallafin kasar Amurka domin ciyar da kasar gaba ta fannonin wasannin kwaikwayo ko finafinai Najeriya irin su Nollywood.

Minista Lai Mohammed ya ce Najeriya ta kashe makudan kudade wajen tallafawa fannonin aladuna da kimiyar sadarwa da biliyoyin naira domin cigan kasa.

Ministan yayi anfanin da wannan damar wajen kare matakin da Najeriya ta dauka a kwanakin baya na haramta ayyukan kafar sadarwar Twitter.

Tuni dai gwamnatin ta dage wannan haramci bayan da kanfanin Twitter ya amince da wasu sharudda da gwamnatin Najeriya ta gindaya mata.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:04 0:00

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG