Bayan sun sha fama na kusan tsawon shekaru biyu, jami'an sun fito daga wata ganawar da su ka yi A Vienna kasar Austria, na nasarar cimma yarjajjeniya ta takaita shirin nukiliyar Iran a madadin dage mata takunkumin tattalin arziki mai tsanani.
Zuwa yau wannan yarjejjeniyar na aiki kuma ana ganin sakamako muraran a muhimman sassanta; to amma har yanzu bangarorin biyu na dan shakkar juna cewa dayan na iya amfani da yanayin da yarjajjeniyar ta samar don cimma wata manufa a maimakon kiyaye sharuddan da su ka wajaba kansa.
Shugaba Obama ya kira yarjajjeniyar nasara, ya kara da cewa, "An dakile hanyoyin Iran na kaiwa ga mallakar makamin nukliya." Ya ce wannan yarjejjeniyar, wadda aka aiwatar a watan Janairun da ya gabata, ta tsawaita lokacin da zai dauki Iran kafin ta iya kirkiro makamin nukiliya daga wata biyu ko uku zuwa wajen shekara guda.
To amma masu sukar yarjajjeniyar har yanzu ba su canza hasashensu na cewa yarjajjeniyar ba za ta iya sa Iran ta daina take-takenta na soji a Gabas Ta Tsakiya ko kuma ta hana Iran iya kirkiro makamin nukiliya ba.