A wata sanarwa da hukumar NAPTIP ta aikawa Muryar Amurka an ce wannan matar mai safarar mutane ta kasa da kasa mai suna Joy Shandy Okah ‘yar Najeriya, an cafke ta ne a birnin na New Delhi aka ceto wasu yara mata guda uku da ta kai su kasar Indiyan ta kuma tilasta masu yin karuwanci.
Bisa ga bayanin hukumar, kafin dauko su daga Najeriyam sai da mata ta sa ‘yan matan suka yi rantsuwa kafin ta kaisu India, sannan bayan sun isa can kuma ta kwace wayoyin salularsu da takardun bulaguronsu.
Matar ta tilastawa ‘yan matan wadanda aka tabbabar sahihancin takardun bulaguron nasu ‘yan asalin jihohin Cross Rivers da Edo ne a kudu maso kudancin Najeriya, biyanta Naira miliyan hudu da dubu dari biyar kowacce ta hanyar yin karuwanci kafin jami'ai su kubutar dasu. ranar shida ga watan Fabrairu na wannan shekara.
Tuni kuma ‘yan sandan birnin Delhi suka kammala bincike nan take inda kasa da awa asahirin da hudu aka gurfanar da ita gaban kotu don fuskantar shari'a.
Lamarin ya ja hankalin masu fafutuka irin su Halima Nuruddeen e kwarriya kan halayyar bil'adama, wacce ke cewa akwai bukatar a daga murya don kawo karshen wannan matsala duk da cewa gwamnati a nata bangaren na iya bakin kokarinta.
Shima jagoran cibiyar CAJA mai rajin neman kyakkyawan shugabanci a Najeriya Comrade Kabir Dakata na mai cewa wasu ‘yan Najeriya sun maida fataucin mutane babban masana'antar dake kawo masu kudi,don haka akwai bukatar hada karfi da karfe don tunkarar matsalar
Saurari rahoto cikin sauti daga Hassan Maina Kaina:
Your browser doesn’t support HTML5