Wata kididdiga daga ofishin jihar Kano na hukumar NAPTIP mai yaki da fatauci da bautar da bil’adama a Najeriya ta nuna cewa, a cikin makonni hudu da suka gabata, jimullar mutum 117 jami’an hukumar suka ceto daga hannun wadanda ke yunkurin safarar su zuwa kasashen Libya da Faransa da kuma Italiya.
Hukumar ta NAPTIP dai ta ce masu yunkurin fataucin mutanen sun so yin amfani da barayin hanyoyi ne a jihohin Jigawa da Katsina domin safarar wadannan mutane wadanda galibin su samari ne da ‘yan mata kuma 80 daga cikin su anyi nasarar kubutar da su ne bisa tallafin jami’an ‘yan sandan Jamhuriyar Nijar.
Mohammed Ali Mashi tsohon kwamandan shiyya a hukumar NAPTIP ya ce wannan dabi’a ta safarar mutane a duniya shi ne na uku ta hanyar samun gurbataccen kudi masu kazamar riba.
Sai dai hukumar ta NAPTIP ta ce baya ga kubutar da wadancan ‘yan Najeriya 117, jami’anta sun cafke mutum biyar da take tuhuma da hannu wajen safarar su zuwa ketare.
Malam Abdullahi Babale kwamandan hukumar mai kula da shiyyar Kano ya ce an ba su ikon su bi kiddigar wannan lamari kuma Allah ya ba su nasara.
Amma Mohammed Ali Mashi ya ce akwai bukatar kasashen Afrika ta Yamma su samar da doka ta bai daya domin tunkarar wannan kalubale.
Binciken hukumar NAPTIP ya nuna fatara da talauci da kuma rashin aikin yi na cikin jerin matsalolin da miyagu ke amfani da su wajen yaudarar samari da ‘yan mata a Najeriya su yi safarar su zuwa ketare.
Saurari rahoto cikin sauti daga Mahmud Ibrahim Kwari:
Your browser doesn’t support HTML5