Rahotanni daga jihar Nejan Najeriya na cewa, ‘yan bindigar da suka sace daliban makarantar Salihu Tanko Islamiyya da ke Tegina a karamar hukumar Rafi sun sako su.
Shugaban karamar Hukumar Rafi Alh.Isma'ila Modibbo ya tabbatar da cewa an sako yaran su 93 a cikin daren Alhamis wayewar garin jumma;a kamar yadda ya yi wa wakilin Muryar Amurka Mustapha Nasiru Batsari karin bayani ta wayar salula.
"Yara dai Allah ya taimaka an yi bakin kokari, yara sun zo hannu, ga su nan su 93, babu ko daya da ya mutu, ga su nan za mu kai su asibiti."
Modibbo ya kuma fayyace cewa adadin daliban su 93 ba 130 da ake ta yayatawa ba.
Sakin daliban na zuwa ne sama da wata biyu bayan da aka yi garkuwa da su a karshen watan Mayu.
"Alhamdulillahi, yau bakin cikinmu ya zama darıya, yaranma sun dawn, mun godewa Allah." Malama Asabe Shehu Daya Daga dikin iyayen yaran ta adawa Muryar Amurka.
Jim kadan bayan sace daliban, ‘yan bindigar suka sako 11 daga cikin su saboda karancin shekarunsu.
Iyayen daliban sun biya kudin fansa na miliyoyin nairori amma duk da haka ba sako daliban ba.
Wasu rahotanni sun ce har sai da aka sayar da wani sashe na makarantar wajen hada kudaden fansar.
Akan daura alhakin matsalar garkuwa da mutane don neman kudin fansa ne akan ‘yan fashin daji wadanda ya zuwa yanzu kididdiga ta nuna sun sace sama da dalibai 1,000 tun daga watan Disamba bara.
Kamar Kaduna, jihar Neja wacce ke makwabtaka da ita na fama da matsalar ‘yan bindiga wadanda kan kai hare-hare a kauyuka da garuruwa.
Ko a ranar Laraba ma gwamnan jihar Abubakar Sani Bello da ke mulki karkashin jam’iyyar APC, ya kai ziyara garin Ma’undu da ke karamar hukumar Mariga, wanda ya zama kufai saboda al’umarsa ta tsere domin kaucewa hare-haren ‘yan bindiga.
Saurari cikakken rahoton Mustapha Nasiru Batsari:
Yadda Daliban Da Aka Sako A Najeriya Suka Hadu Da Iyayensu Cikin Yanayi Mai Sosa Rai