Bukatar gwamnatin Nigeria ta dauki mataki ko kuma matakan zakulo masu daukan nauyin masu karkashe mutane ya kara yawa, bayan wata sanarwar da dan majalisar wakilai Ahmed Idris Wase ya gabatar cewa, akwai wasu ‘yan siyasa dake haddasa da rikici, musamman tsakanin makiyaya da manoma.
Ahmed Idris Wase ya ce wannan ikirari yana kunshe cikin wani rahoton da suka baiwa gwamnatin Plato. Ya ce suna da shedarcewa mutane fiye da dari uku aka tura kasar Israila, domin samun horo akan karkashe mutane.
Yace zai baiwa kakakin majalisar Yakubu Dogara wannan rahoto. Ahmed Idris Wase ya ce akwai masakan makamai hudu da aka kai yankin arewa ta tsakiya aka zabawa ‘yan siyasa masu tada fitina.
Shugaban JIBWIS Shaikh Abdullahi Lau ya bukaci majalisa ta binciki rahoton domin katse hanzarin masu tada fitina. Yace idan an bincika an kuma gano ko su wanene, to ya kmata a hukunta su. Idan ba haka aka yi ba, tamkar an ba kowa lisisin ya dauki doka a hannunsa ne.
Shi ma shugaban matasa na kungiyar Kiristoci reshen arewa mai bishara Musa Misal ya ce lallai baragurbin ‘yan siyasa na yin anfani da matasa, yana cewa shi dan siyasa idan yana neman kujera bai damu da wanda zai mutu ba muddin ya samu kujerar. ‘Yan siyasa zasu zuga matasa su yi ba daidai ba tare da yi masu alkawarin azurtasu amma da zara ya ci sai ya yi watsi dasu. Ya yi kiran a yi taka tsan tsan da irin wadannan ‘yan siyasa masu yaudarar matasa.
Shaikh Bala Lau ya bukaci duk mabiya addini a Nigeria su zauna da juna lafiya, cikin mutunci saboda babu wanda zai kori wani daga kasar, musulmi ko kirista.
A saurari rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya
Your browser doesn’t support HTML5