Rahotanni dai na cewa wasu gungun mahara ne suka farma wasu kauyukan Fulani biyar dake karamar hukumar Lau,inda aka kona gidaje,sace shanu baya ga rayukan da aka rasa.
Su dai wadannan yan gudun hijira da aka sarinsu mata ne da kananan yara,yanzu haka sun ba zama ne zuwa Jalingo fadar jihar da kuma wasu yankunan dake makwabtaka da inda aka kai hare haren,kuma kawo yanzu ma tuni direbobi suka daina bin hanyar Numan zuwa Mayo-Lope inda lamarin yafi shafa.
A wajen wani taron manema labarai a Jalingo,shugaban kungiyar Miyetti Allah a jihar Taraba Jauro Sahabi Mahmud Tukur ,yace abun dake faruwa yakai halin ha’ula’I dake bukatar daukin gwamnatin Tarayya. Ya ce a tsakiyar dare mahaura suka zagaya suka shiga kauyukan Fulaninsu da duk inda aka sani a mazaunin makiyaya sun kashesu sun kona masu gidaje sun kuma kasha shanu babu gaira babu dalili. A cewarsa sun sace shanu sun fi dari biyar.
Shaidun gani da ido sun ce kawo yanzu fiye da mutum 20 aka yiwa jana’iza,yayin da ko rundunan yan sandan jihar ta bakin kakakinta,ASP David Misal wanda ya tabbatar da hare haren da aka kai,ya ce kawo yanzu mutum guda aka kama ,kuma mutum shida ne suka mutu.
To sai dai kuma ya zuwa lokacin aiko da wannan rahoto wasu majiyoyin tsaro sun bayyana cewa an sami cafke wasu da ake zargi da hannu a wadannan hare hare.
A saurari rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani
Facebook Forum