Muna aiwatar da umarnin shugaban kasa na shekarun kudi na 2017 da 2018 na kawo karshen taimakon kasashen waje da ake baiwa kasashen guda uku na nahiyar Amurka, inji mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen a cikin wata sanarwa, yana mai cewa zamu tattauna da majalisun tarayya a kan wannan batu.
Kasashen uku na arewacin kasashen tsakiyar Amurka da ake musu lakabi da Northern Triangle, da suka hada da Guatemala, Honduras and El Salvador an shirya basu taimakon kudi dala miliyan 500 a shekarar 2018 da kuma sauran ragowar miliyoyin dala da yakamata a basu a shekarar 2017, a cewar jaridar Washington Post.
Wannan matakin na zuwa a lokacin da shugaban na Amurka Donald Trump, yace kasashen sun shirya ayarin bakin haure da suke zuwa nan Amurka.