Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Shirin Kakabawa Venezuela Takunkumai


Trump
Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya fadawa ‘yan jarida a jiya Juma’a cewa kasar Venezuela na fama da tsananin matsaloli, yayin da wasu jami’an fadar White House suka kyankyasa batun kakabawa kasar takukuman tattalin arziki.

Trump ya amsa tambayoyin manema labarai a kan batutuwa da dama a jiya Juma’a da rana, ciki har da batun matakan da Amurka zata dauka a kan kasar ta Venezuela.

Venezuela na fama da matsaloli inji Trump, yana mai cewa, babu wutar lantarki ba mai da motoci zasu yi aiki da shi a kasar. Yace idan kana tunanin bin tafarkin gurguzu ne, to ka dubi kasar Vebnezuela.

Tun da safiyar jiya ne manzon Amurka na musamman a Venezuela, Elliott Abrams, yace sakataren harkokin wajen Mike Pompeo yana rike da jerin matakan da akwai yiwuwar daukar su, ciki har da takunkuman tattalin arziki domin kasancewar sojojin Rasha a Venezuela.

Jiragen yakin Rasha guda biyu sun isa wajen birnin Caracas a ranar Asabar waccan mako kuma ana zaton akwai sojojin Rasha da kayan aikin su a cikin jiragen.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG