Wata sanarwa da sashin hulda da jama'a na ofishin jakadancin Amurkan dake Najeriya ya fitar na nuna cewa, duk wani dan Najeriyar da ya cancanta kuma ya cika ka'idojin da aka tsara to za a bashi takardar izinin yin bulaguro Amurka.
Tuni kuma wannan ya fara jan hankalin masana da kwararru a Najeriyar kan Alfanu ko akasin hakan, inda masanin siyasar kasa da kasa kuma babban malami a jami'ar Abuja Dr. Farouk BB Farouk ke cewa wannan mataki ne da ya dace kuma yazo lokacin da ya dace.
Bisa ga cewar shi, wannan mataki zai taimaka musamman ga mutanen dake da wata hidima na ilmi ko harkar neman lafiya ko kasuwanci a Amurkan.
Amma kwararren Jami'in Diflomasiyya Ambasada Sulyman Dahiru ya ce koda yake wannan mataki na gwamnatin Amurka yayi daidai to amma yayi zargin cewa akasarin ‘yan Najeriya dake rububin neman takardun izinin shiga Amurkan basu da wani dalili mai karfi.
Ambasada Dahiru yace yawancin yan Najeriya dake son zuwa Amurkan suna zuwa ne kurum don nuna isa ganin sau tari bai wuce batun shakatawa ko haihuwa ne ke kaisu don jariran su sami takardun PASSPORT na Amurkan, al'asmarin da yayi kira ga Amurkan da ta sake tsari.
Saurari rahoto cikin sauti daga Hassan Maina Kaina:
Your browser doesn’t support HTML5