Rundunar tsaron Amurka ta “U.S Marshals” ta kara sunan dan Najeriya da hukumomin jihar Rhode Island ke tuhuma da laifuffukan kisan kai, tare da haddasa mummunan rauni ga wani karamin yaro, da arcewa domin gudun shari’a a cikin jerin mutane 15 da take nema ruwa a jallo.
Ta kuma sanya ladan da ya kai dala 25, 000 ga duk wanda ya bada labarin da zai kai ga kama shi.
A cewar wani rahoto a shafin yanar gizon rundunar tsaron, ana tuhumar Olalekan Abimbola Olawusi, mai shekaru 48, da laifin kisan kai da kuma wasu laifuffukan 2 na haddasawa karamin yaro mummunan rauni bayan da wani jami’in bada agaji a lardin Providence ya samu dansa da munanan raunuka a wani gida a ranar 3 ga watan Afrilun 2017.
An garzaya da yaron zuwa asibiti da lalurar tsayawar bugun zuciya dake bukatar a sake tayarwa domin ci gaba da aiki.
Binciken likitoci a asibitin ya nuna raunuka 18 da suka fara warkewa, dake nuna cewa an jima ana cin zarafin yaron.
Raunukan sun hada fashewar kokokn kai, da taruwar jini a kwakwalwa, da mummunan rauni a kwakwalwar da karaya a hakarkari da kwala da kafafuwa da hannaye. duk da an dora shi akan injin dake tallafawa rayuwa, yaron ya mutu cikin akuba bayan watanni 6.
Da fari ‘yan sandan lardin Providence sun kama tare da tuhumar Olawusi da laifin cin zarafin yaro karami a ranar 20 ga watan Afrilun 2017. An sakeshi a wannan rana sai dai ya arce daga bisani.
Sakamakon mutuwar yaron a ranar 31 ga watan Oktoban 2017, an mayar da tuhumar zuwa kisan kai.