Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mayakan FPL Tara Sun Mika Wuya Ga Gwamnatin Sojin Nijar


Sojojin Juyin Mulkin Nijar
Sojojin Juyin Mulkin Nijar

Mambobin kungiyar ‘yan tawaye tara dake neman a sako hambararren shugaban kasar Nijar sun mika wuya a jiya litinin, kamar yadda jami’an kasar da sojoji ke mulka suka bayyana.

An kafa kungiyar ‘yan tawayen Patriotic Liberation Front (FPL) a watan Agustan shekarar 2023, wata guda bayan hambarar da zababben shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum a wani juyin mulki da sojoji suka yi.

Tun a wancan lokaci Bazoum na tsare da matarsa Hadiza a fadar shugaban kasa da ke Yamai babban birnin kasar.

Gwamnan Agadez, wani jami'in yankin hamadar arewacin kasar dake kusa da kasar Libya ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa, mayakan FPL tara sun tuba tare da mika makamansu da alburusai a ranar litinin a yayin wani biki a gaban Janar Ibra Boulama.

Mambobin FPL sun fara mika wuya ne a farkon wannan wata bayan tattaunawa mai ma'ana da wasu masu fada aji na kasar, kamar yadda kafar yada labarai ta Air-Info ta ruwaito.

A ranar 1 ga watan Nuwamba mai magana da yawun FPL Idrissa Madaki tare da wasu mambobi uku sun mika kansu a lokuta daban-daban a wasu garuruwa biyu da ke kusa da kan iyakar kasar Libya, kamar yadda sojojin Nijar da gidan talabijin na kasar suka bayyana.

A makon da ya gabata, an cire wa shugaban FPL Mahmoud Sallah, da kuma wasu mutane bakwai na gwamnatin Bazoum da ake zargi da kai hare-haren ta’addanci. 'yancin zama 'yan kasa na dan lokaci,

Sallah ya dauki alhakin kai hare-hare kan sojoji a arewa da kuma lalata wani muhimmin bututun mai da ke dauke da danyen mai zuwa Benin a watan Yuni. Ya kuma yi barazanar kai hari a wurare masu mahimmanci.

Wata kungiyar ‘yan tawayen da ita ma ta ke neman a sako Bazoum, da ake kira, "Patriotic Front for Justice" (FPJ), tana tsare babban jami'in hukumar soji ta yankin arewa maso gabashin Bilma da wasu jami’an tsaronsa hudu, wadanda aka yi garkuwa da su bayan wani kwanton bauna a tun watan Yunin da ya gabata

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar da ke fama da hare-haren kungiyoyin masu da'awar jihadi, a 'yan makonnin da suka gabata sun kara tsaurara matakan tsaro, inda sojoji ke sintiri da bincike da kuma binciken ababan hawa.

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG