Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bashin Da Ake Bin Najeriya Ya Haura Dalar Amurka Biliyan 42.9-DMO


Dalar Amurka
Dalar Amurka

Wani rahoto da ofishin kula da basussuka da kuma rance a Najeriya DMO, ta fitar, ta ce bashin da ake bin kasar a karshen watan Yunin shekarar 2024, ya haura dalar Amurka biliyan 42.9, kwatankwacin Naira tiriliyan 71,826,183,000,000

Cikin tarin basussukan da ake bin kasar dai, akwai na Gwamnatin tarayyar kasar da ya kai dala biliyan 38, inda jihohin kasar har da babban birnin tarayya Abuja, ake bin su bashin dala biliyan 4.89 wanda shima kwatankwacin sa ya kai Naira tiriliyan 8,187,180,300,000, sai kuma wasu basussukan cikin gida da ake bin jihohin da ya kai Naira tiriliyan 4.27.

Cikin kunshin basussukan dai akwai na Bankin Duniya da kuma Asusun bada Lamuni na IMF da suka kai Dala biliyan 17.13, sai kuma na tarayyar Turai da ya kai Dala biliyan 15.12, ɗaiɗaikun kasashen duniya da kuma Bankuna su kuma suna bin kasar bashin Dala biliyan 5.49.

Cikin basussukan da ake bin jihohin kasar dai, jihar Legas ce ke kan gaba, inda kudin da ake binta ya haura dala biliyan 1.2, sai kuma jihar Kaduna dake biye da bashin dala miliyan 640.99.

Hakazalika basussukan cikin gida da ake bin jihohin kasar Legas ce ke kan gaba inda ake bin ta bashin Naira biliyan 885.99, sai kuma jihar Rivers da bashin Naira biliyan 389.2.

A hirarsa da Muryar Amurka, Farfesa Kabir Isa Dandago malami kuma masanin tattalin arziki dake Jami’ar Bayero a jihar Kano, ya ce “babban dalilin da yasa basussukan da ake bin Najeriya na ci gaba da hauhawa, shine Gwamnatin kasar ta dogara ne wajen karbar bashi domin yin ayyukan raya kasa, saboda kudaden shigarsu bai taka-kara-ya-karya ba. Idan har Gwamnatocin jihohi da na tarayya suka karbi basussukan suna bigewa ne wajen yin facaka da kudaden, bawai ana aiwatar da su bane ta hanyar da suka dace.

Dr. Isa Abdullahi Kashere, masanin tattalin arziki dake Jami’ar Kashere a jihar Gombe, ya ce “Gwamnatocin jihohin na amfani da salo dayawa wajen karbar irin wannan bashi, kuma hakan yana yi wa tattalin arzikin kasar illa ta yadda kasafin kasar na tafiya gaba daya wajen biyan basussukan.

Kasar dai ta kashe Dala biliyan 10 a shekarar 2023 wajen shigowa da kayan abinci kasar, a cewar Bankin Raya Nahiyar Afirka (AfDB) wanda masana na ganin wani babban gibi ne dake kassara tattalin arzikin kasar idan aka kwatanta yadda kasar ke da dimbin arzikin albarkatun noma.

Saurari cikakken rahoto daga Rukaiya Basha:

Bashin Da Ake Bin Najeriya Ya Haura Dalar Amurka Biliyan 42.9.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:49 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG