Amurka Ta Tuhumi Wasu Jami'an Leken Asirin Rasha Bakwai

Ma'aikatar Shari'ar Amurka, jiya Alhamis ta bayyana cewa ta huhumi wasu jami'an leken asirin Rasha su 7 da laifin kutsen komfutocin cibiyoyin yaki da muggan kwayoyi na kasa da kasa, da kuma kungiyoyin da ke binciken amfani da guba da ake zargin kasar ta Rasha da yi.

Da ya ke bayyana tuhume-tuhumen a birnin Washington, Mataimakin Attoni-janar John Demers ya ce 'yan Rasha din da ake tuhuma ma'aikatan hukumar leken asirin sojojin Rasha ne, GRU a takaice, kuma a baya Mai Bincike Na Musamman kan katsalandan din da ake zargin Rasha da yi, Robert Mueller, ya tuhumi mutane ukun kan batun kutsen komfutocin jam'iyyar Democrat a lokacin zaben Shugaban kasar Amurka na 2016.

To amma Demers, wanda shi ne shugaban sashin tsaro na ma'aikatar, ya ce tuhume-tuhume na baya-bayan nan ba su da alaka da binciken da Rasha ke yi kan katsalandan din da ake zargin Rasha da yi a zaben Amurka na 2016.